Gwamna APC a Arewa ya Tona Asirin Masu Daukar Nauyin Ta'addanci a Jiharsa

August 2024 · 3 minute read

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Binuwai - Gwamnan Binuwai, Hyacinth Alia ya shiga damuwa saboda kamarin da ta'addanci ke yi a jiharsa, wanda ke jawo asarar rayuka.

Gwamnan ya bayyana cewa wasu tsirarun 'yan siyasa da ke zamansu a babban birnin tarayya, Abuja ne su ke daukar nauyin kashe jama'ar jiharsa.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da kuka da mulkin APC, 'yan majalisa 3 a Arewa sun sauya sheka zuwa daga PDP

Jaridar Vangaurd ta wallafa cewa gwamna Alia ya ce ana kashe mutane babu kakkautawa a yankunan da ke Sankera da Katsina-Ala, Ukum da Logo a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu na kokarin kawar da ta'addanci," Gwamnati

Gwamnan Binuwai, Hyacinth Alia ya bayyana takaicin yadda 'yan jihar ke kashe 'yan uwansu a wurare daban-daban da sunan ta'addanci, Jaridar Independent ta wallafa.

Ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala taron addu'a a cocin da ke gidan gwamnatin jihar, inda gwamnan ya ce su na kokarin shawo kan matsalar.

Gwamna Alia ya kara da tunatar da jama'a cewa a lokacin gangamin neman zabensa, ya dauki alkawarin hana kashe-kashe a jihar, kuma har yanzu su na kan bakarsu.

"Akwai ta'addanci iri 2 a Binuwai," Gwamna Alia

Gwamna Hyacinth Alia ya ce su na kokarin yakar ta'addanci ta fuskoki da dama a jihar Binuwai; daya daga ciki ita ce ta bakin haure da ke shiga jihar.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri: Ministan Tinubu ya ba 'yan Arewa shawari kan zanga-zangar da ake shirin yi

A cewar gwamnan, dayar kuma ita ce ta 'yan uwan juna wadanda ke zaune a wuri guda musamman a karamar hukumar Ukum da Sankera

Ta'addanci: Gwamnatin Alia za ta yi sulhu?

A wani labarin kuma, gwamnatin Binuwai ta ce ta shiga dimuwa saboda yadda 'yan bindiga ke cikin karensu babu babba tare da salwantar da rayukan jama'a a jihar.

Kwamishinan yada labaran jihar, Mathew Abo ya ce gwamnati na bakin kokarinta wajen kare rayukan jama'a, saboda haka ne ma za ta dauki matakin sulhu da miyagun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYF5hZRmnrCZnaOubsXAZp2apJyWwKJ5zJqqrmWUlsKsrdFmpZqtqZ67bsDAmpudmZ6Ytm6tjJugp62nlrZw